Karya ta jira uwardakinta tsawon kwana 6 a asibiti

A farkon makon nan ne aka sada wata karya da
uwardakinta bayan ta shafe tsawon kwana shida
tana zaune a kofar dakin da aka kwatar da ita a
wani asibiti da ke kasar Spain.
Karyar mai suna Maya, wadda take da shekara
biyu a duniya, ta zauna a kofar dakin da aka
kwantar da uwardakinta mai suna Sandra Iniesta,
’yar kimanin shekara 22 a duniya, har sai bayan
da aka sallame ta daga asibitin mai suna Elda.
Sandra ta yi fama ne da ciwon ciki yayin da suke
tafiya da mahaifinta da kuma karyar a kan
hanyarsu ta zuwa birnin Barcelona.
Daga nan ne suka garzaya asibitin Elda, aka
kwantar da Sandra na tsawon kwana shida, inda
aka yi mata aiki, kamar yadda jaridar The
Independent ta bayyana.
A wannan lokaci ne mahaifin Sandra ya yi
yunkurin komawa da karyar cikin mota don su
koma masaukinsu, amma sai ta yi kememe ta ki
barin kofar dakin da aka kwantar da Sandra.
Wadansu daga cikin ma’aikatan asibitin da suka
fahimci halin da ake ciki, sai suka fara yada
hotun Maya ta shafin sada zumunta na
Facebook. Bayan haka ne, sai jama’a suka fara
tururuwar ziyartar asibitin don yin ido hudu da
Maya, inda wadansu daga cikinsu har da ba ta
kyauta.
Yayin da aka sallami Sandra, manema labarai sun
ji ta bakinta kan al’amarin, inda ta ce hakan ba
wani bakon abu ba ne a gare ta. “Maya ta saba
jira na duk lokacin da na shiga daki, ko
makewayi. Ba ta barin wurin har sai bayan na
fito,”inji ta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Karya ta jira uwardakinta tsawon kwana 6 a asibiti"

Post a Comment