An kai harin bama-bamai a Maiduguri

Rahotanni daga birnin Maiduguri da ke jihar
Borno ta Najeriya na cewa wasu da ake zargi
'yan Boko Haram ne sun kai hari da safiyar ranar
Asabar.
Ganau sun shaida wa BBC cewa bama-baman
guda biyu sun tashi ne a kusa da kofar shiga
sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi da kuma
gidan man NNPC.
Hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA, ta ce
mutum tara sun rasa rayukansu, yayin da mutum
24 suka samu raunuka.
Birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-
haren 'yan kungiyar ta Boko Haram, kodayake
yanzu ba safai ake kai masa hare-hare ba.
Dakarun sojin Najeriya na cewa suna bakin
kokarinsu na kawar da kungiyar ta Boko Haram,
suna masu kira ga mutane cewa su rika kai
rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi
ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kai harin bama-bamai a Maiduguri"

Post a Comment