An yi yamutsi a wasan West Ham da Chelsea

An yi yamutsi tsakanin magoya bayan West Ham
da na Chelsea, bayan da suka tashi a wasan
League Cup a ranar Laraba.
West Ham ce ta doke Chelsea da ci 2-1, wanda
hakan ya sa za ta kara da Manchester United a
wasan daf da na kusa da na karshe a gasar.
Magoya bayan kungiyoyin biyu sun yi ta jifan
junansu da robobin ruwan sha da kwandaloli,
hakan ya sa jami'an tsaro suka kama mutane
bakwai.
Ana ta samun hatsaniya tsakanin magoya baya
tun komawar West Ham United sabon filin
wasanta.
West Ham ta ce za ta hana duk wanda ta samu
da laifi shiga kallon wasa a filin har abada, za
kuma ta yi amfani da na'urar daukar hoton bidiyo
domin gano masu laifi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An yi yamutsi a wasan West Ham da Chelsea"

Post a Comment