Fari ya jefa mutane miliyan 1.5 cikin yunwa a Madagascar

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane kusan
miliyan daya da rabi a kudancin Madagascar na
fuskantar yunwa, sakamakon matsanancin fari.
Hukumar abinci ta MDD ta ce an samu raguwar
kayan amfanin gona, dangin cimaka matuka, a
kudancin katafaren tsibirin.
A wani yanki guda daya, yawan masarar da ake
nomawa ya ragu da kashi 80 cikin dari a wannan
shekarar, shi kuwa yawan rogon da ake girba a
yankin ya kasance kusan rabi kawai aka samu a
bana.
Shinkafa ma ta ragu zuwa kashi 60 cikin dari kan
yadda aka saba girba, a wasu yankunan, inda
hakan ya sa jama'a suka karkata wajen siyo ta
daga waje.
Wannan matsala ta karancin cimaka ta kuma
jawo tashin farashin kayan abinci a tsibirin, yayin
da wasu mutanen suka koma cin 'ya'yan
itatuwan daji, suna kuma sayar da dabbobinsu da
kayan aikinsu na gona domin su rayu, wanda
hakan ke nufin girbin badi shi ma zai kasance
cikin rashin tabbas.
Majalisar dinkin duniya ta ce sama da rabin
mutanen da ke a wannan hali, suna cikin
tsananin matsalar karancin abinci, abin da ke
nufin suna abukatar taimako.
Hukumar abinci da aikin gona ta majalisar dinkin
duniya, wadda ke aiki tare da shirin samar da
abinci na majalisar, ta ce, za ta taimaka wa
jama'a da kananan gonaki a yankunan da farin ya
fi kamari.
Ta ce za ta taimaka da abinci da irin shuka da
kayan aikin gona, domin manoman su ribaci
damunar da ke tafe, wadda za ta fara a yankin a
watan Nuwamba.
Wasu kasashen Afurkan ma sun shiga irin
wannan matsala ta tsananin fari a baya bayan
nan, wadda annobar sauyin yanayi ta El nino ta
kara kamarin matsalar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Fari ya jefa mutane miliyan 1.5 cikin yunwa a Madagascar"

Post a Comment