Kocin Everton Koeman na zawarcin Wayne Rooney

Kocin Everton Ronald Koeman ya ce zai ji dadi
sosai idan kyaftin din Manchester United Wayne
Rooney ya koma kungiyar.
Jaridu da dama sun yi hasashen cewa Rooney,
mai shekara 31, ba shi da makoma a United
bayan da kocin kungiyar Jose Mourinho ya ki
sanya shi a wasa.
Sai dai Koeman ya ce, Rooney "Dan wasa ne mai
kwazo kuma har yanzu yana haskakawa."
Amma Mourinho ya jaddada cewa Rooney -
wanda a yanzu kwallaye uku ne kadai suka hana
shi zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a
kungiyar - yana cikin tsare-tsarensa.
Koeman ya kara da cewa: "Ban san halin da
yake ciki ba, kuma bana son yin katsalandan.
Amma idan Rooney ya dawo Everton za mu ji
dadi."
Rooney ya koma United daga Everton a kan
£27m a shekarar 2004, kuma ya zura kwallaye
246 a wasanni 532 da ya buga.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kocin Everton Koeman na zawarcin Wayne Rooney"

Post a Comment