*DUNKULALLUN SAKONNI WADANDA SUKA KUNSHI MAS'ALOLI SHA BIYU NA AQIDAHDA FIQHU DA MU'AMALA*

            *🖨FITOWA TA BIYAR🖨*

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

*TAMBAYA*
_Menene Rukunnan Musulunci?_

*AMSA*

_✏ Tsayuwa Idan Akwai Ikon tsayawar. Amma Wannan a Sallar Farillah ne Kawai._

_✏ Kabbarar Harama. Mutum Zai ce: *"Allahu Akbar"* Fadin Wani Abu ba Wannan ba Bazai Wadatar dashi ba._
_✏ Karatun Fatiha a Kowace Raka'a_
_✏ Ruku'u_
_✏ 'Dagowa daga Ruku'u_
_✏ Daidaituwa a tsaye Bayan Dagowa daga Ruku'u_
_✏ Sujjadah_
_✏ 'Dagowa Daga Sujjadah_
_✏ Zama tsakanin Sujjadai Biyu_
_✏ Natsuwa a Cikin Dukkan Rukunnai_
_✏ Tahiya ta Karshe_
_✏ Zama Domin Tahiyar_
_✏ Sallama Guda Biyu_

*TAMBAYA*
_Meye Hukuncin Wanda Yabar Rukuni Daga Cikin Wadannan Rukunnan?_

*AMSA*
_Duk Wanda Yabar Rukuni Daya Daga Cikin Rukunnan Sallah, Sallar sa ta 6aci baza'a Kar6a ba._

*TAMBAYA*
_Menene Wajiban Sallah?_

*AMSA*
_✏ Dukkan Kabbarori In Banda Kabbarar Harama._
_✏ Fadin *"Subhana Rabbiyal Azeem"* Sau Daya a Ruku'u._
_✏ Fadin *"Sami'Allahu Liman Hamidahu"* Ga Liman da Kuma Mamu a Yayin Dagowa Daga Ruku'u._

_✏ Fadin *"Rabbana wa Lakal Hamd"* ga Liman da Kuma Mamu Bayan Dagowa daga Ruku'u._
_✏ Addu'a tsakanin Sujjadah Biyu *"Rabbig Firli, Rabbig Firli"*
_✏ Tahiya ta Farko_
_✏ Zama Domin Tahiya ta Farkon_

*TAMBAYA*
_Meye Hukuncin Wanda Yabar Wajibi daga Cikin Wajiban Sallah?_

*AMSA*
_Duk Wanda Yabar Wajibi Daga Cikin wajiban Sallah da Mantuwa, Zai Sujjada Biyu na Rafkanuwa._

*TAMBAYA*
_Wane Abubuwa ne Suke 6ata Sallah?_

*AMSA*
_✏ Ci da Sha da Gan-gan_
_✏ Maganar da bata Gyaran Sallah ba da Gan-gan_
_✏ Barin Rukuni ko Sharadi da Mantuwa koda Gan-gan._
_✏ Dariya Idan takai ga Kyakyacewa_
_✏ Rashin Jeranta Salloli Yanda suke. Kamar Ya farayin La'asar Sannan Azahar._
_✏ Kaucema Alqibla da Dukkan Jiki._
_✏ Fitar Iska ta Dubura_
_✏ Yawan Waige-Waige ba tare da wani Dalili ba._
_✏ Riga Liman yin Daya daga Cikin ayyukan Sallah da gan-gan._


_Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Fitowa ta Gaba_

*"سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاإِلَهَ إلاّ اللَّه، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيكَ"*

_*✍🏽✍🏽✍🏽Yahya Sulyman✍🏽✍🏽✍🏽*_
                     *{Baban Abbah}*

_MAI SHA'AWAR SHIGA GROUP DIN YA TURO SUNANSA TA WHATSAPP:_
_*+2348034643244*_
_*+2348089074217*_

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "*DUNKULALLUN SAKONNI WADANDA SUKA KUNSHI MAS'ALOLI SHA BIYU NA AQIDAHDA FIQHU DA MU'AMALA* "

Post a Comment