[Android] YADDA ZAKA SAWA KOWANE IRIN VIDEO ko FILM SUBTITLE A WAYAR ANDROID

Kamar yadda kuka sani subtitle shine wannan Rubutun da yake fitowa a kasan video/film yayin da ake kallo wato shi wannan Rubutun yakan taimaka mu fahinci film yayin da muke kallonsa koda wannan film din ba yaran mu bane domin mafi yanwancin subtitle zaka tarar da turancine koda kuwa film din bana turanci bane, sabo da haka wannan de rubutun shi ake kira da subtittle wanda duk maganar da akayi a film din zasu Rubuta ta a kasan film din ta yadda zai taimakawa mai kallon film din ya fahinci film din sosai da sosai, wannan shine abin da ake kira da subtitle Idan ka lura mafiya wayan video film da muke kallo a wayoyinmu na android basu fiya zuwa da wannan subtitle dinba sabo da haka daga yanzu idan kanaso ka sanyawa video domin ka kara fahintar film din to ga yadda zakayi, : Da farko ka tabbata kana da MX player idan kuma baka da ita to sai kayi download dinta Sannan ka nemo subtitle na video din da kakeson ka dorawa, domin nemo subtitle din sai kaje google ka rubuta download subtitle for sunan film din da kakeso dorawa , idan kayi haka zasu baka wannan wanda ka nema din to zaka ganshi a .srt wani kuma a .zip to saika nemi explore kayi extract dinsa bayan kayi extract dinsa sai kaje ka ajiyeshi a folder ta dabam wanda ka gadama, sannan saikaje ka bude MX player ka nufi inda video/film dinka yake sai kayi click akansa zakaga ya farayi kamar yadda ka saba amma subtitle bai hauba, to karka damu kawai ka danna option na wayarka saika shiga Inda aka Rubuta daganan saika shiga idan ya bude zaka (Folder Up) saika shiga nan kaje folder daka ajiye subtitle dinka sai kayi click akansa shikkenan nan take zakaga ya hau zakaga video ka yana bayyanama wannan Rubutun na kasa, Idan kuma kanaso zaka iya chanja Rubutun zuwa yaran da ranka ya keso daga english zuwa hausa kokuma zuwa duk yaran da kayi niya domin yin hakan sai ka nemi explore ko es explore kokuma root explore saika bude kaje inda subtitle yake saikayi extract dinsa daganan kayi open dinsa as txt saika chanja duk abin da kakeso sannan kayi save dinsa sai kaje kabi hanyar dana bayar ta farko ta sama domin dorashi Allah ya basa sa,a

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "[Android] YADDA ZAKA SAWA KOWANE IRIN VIDEO ko FILM SUBTITLE A WAYAR ANDROID "

Post a Comment