Nigeria: Za a yi bincike kan lalata da 'yan gudun hijira

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya umarci
a gudanar da binciki kan zargin yin lalata da
'yan gudun hijirar Boko Haram da kungiyar
Human Rights Watch (HRW) ta yi.
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce
shugaban ya kadu da jin wannan labari.
Sannan ya ce "kyautata jin dadin rayuwar
wadannan mutane da ke fuskantar barazana abu
ne mai muhimmanci ga gwamnatinsa".
Sanarwar wacce mai magana da yawun
shugaban, Garba Shehu ya sanya wa hannu, ta
ce 'yan Najeriya dama kasashen duniya su san
cewa gwamnati ba za ta dau zargin na kungiyar
ta HRW da wasa ba.
Shugaba Buhari ya bai wa babban Sipeton 'yan
sandan kasar da gwannonin jihohin da lamarin ya
shafa umarnin su gaggauta gudanar da bincike
game da batun.
Binciken na su shi zai nuna mataki na gaba da
gwamnatin za ta dauka, a cewar sanarwar.
A ranar Litinin ne kungiyar HRW ta zargi wasu
jami'an gwamnatin Nigeria da yin lalata da 'yan
matan da rikicin Boko Haram ya raba da
muhallansu, ta hanyar yi musu fyade da
yaudararsu don yin lalata da su.
Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin da rashin yin
abin da ya kamata wajen kare irin wadannan
matan.
Ta kara da cewa ta samu bayanin yin lalata da
kuma fyade kan mata da 'yan mata 43 da ke
zaune a sansanonin gudun hijira bakwai da ke
Maiduguri, a jihar Borno.
Sama da mutane miliyan biyu ne suka bar
gidajensu sakamakon rikicin na kungiyar Boko
Haram.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Za a yi bincike kan lalata da 'yan gudun hijira"

Post a Comment