Hukumar FA ta tuhumi Jose Mourinho

Hukumar kwallon kafa ta
Ingila (FA), ta tuhimi
kocin Manchester United Jose Mourinho kan
ikirarin da ya yi cewa abu ne mai wahala ga
alkalin wasa Anthony Taylor ya iya hura wasan
da United ta yi da Liverpool.
Mourinho ya kara da cewa nada Taylor domin ya
yi alkalancin wasan da suka yi ranar 17 ga watan
Oktoba ya matsa masa lamba.
Dokar kwallon kafa dai ta hana koci ya yi tsokaci
kan alkalin wasa gabanin a yi wasan.
Yanzu dai an bai wa Mourinho wa'adin ranar 31
ga watan Oktoba domin ya yi bayani kan wannan
hali mara kyau da ya nuna, lamarin da ya
kaskantar da wasan kwallo.
Taylor ya bai wa 'yan wasa ruwan-dorawar kati
sau hudu a wasan da suka tashi 0-0.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hukumar FA ta tuhumi Jose Mourinho"

Post a Comment