Facebook ya bude wani sabon dandali

Kamfanin sadarwa na Facebook ya bude wani
sabon dandali, wanda zai bai wa wasu
kamfanoni damar kafa tasu manhajar, domin
kasuwanci.
Manhajar, wadda ke kama da ta Facebook, na
dauke da na'urorin daukar bidiyo da tura
sakwanni.
Sai dai kuma ba a hade suke wuri guda da
sashen da ke nuna sunan mutum da wasu
abubuwa na kashin kansa ba.
An tsara manhajar ne domin ta maye gurbin
wasu manhajojin da ake amfani wajen kasuwanci
kamar manhajar tura sakwannin email.
Wani mai sharhi dai ya ce wannan sabon dandali
zai fuskanci kalubale daga sauran kamfanoni
irinsa da suke gogayya da shi.
Za a sa manhajar a kasuwa domin gogayya da
wasu manhajojin kamar Yammer ta Microsoft,
masu hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin sada
zumunta.
Da kuma manhajar Slack, wadda ake amfani da
ita wajen tura sakwanni.
Wani jami'i a Lewis Consultancy ya ce "Ba wai
samar da hanyoyin kasuwanci ta sada zumunta
ba ne kadai, zai ba su damar gogawa da wasu
manhajojin kamar Google Cloud."
Ana dai amfani da Google Cloud ne wajen
musaya da gyara bayanai.
Ya kuma kara da cewa, "Zai ratsa wurare da
dama a matsayin abu muhimmi guda daya."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Facebook ya bude wani sabon dandali"

Post a Comment