Barcelona ta yi karar shugaban La Liga

Barcelona ta yi karar shugaban gudanar da gasar
La Liga, Javier Tebas, gaban babbar kotun
wasanni ta Spaniya, bayan da ya tuhumi 'yan
wasanta a karawar da suka yi da Valencia.
Tebas ya ce Barcelona na da laifin tada yamutsi
a karawar da ta ci Valencia 3-2 a wasan da suka
yi a ranar Asabar, ta wajen yadda suka dunga
yin murnar kwallo na uku da suka ci.
Hukumar ta La Liga ta ci tarar Valencia fam
1,340, bayan da magoya bayanta suka dunga
jifan 'yan wasan Barcelona da robar ruwan sha.
Shi ma kwamitin da'a na hukumar ya soki rawar
da Barcelona ta taka a wajen yin murnar cin
kwallon, inda ya kara da cewar hakan ne ya
harzuka magoya bayan Valencia.
Barcelona ta ce wadannan kalaman ba su dace
ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Barcelona ta yi karar shugaban La Liga"

Post a Comment