Antarctic: An cimma yarjejeniyar kare halittun ruwa

An cimma wata yarjejeniya da aka dauki shekaru
masu yawa ana tattaunawa, da za ta samar da
yanki mafi girma na duniya da zai kare halittun
ruwa a tekun Antaktika.
Kasashen Amurka da New Zealand ne za su kula
da ikon yankin sama da murabba'in kilomita
miliyan daya da rabi.
Yankin da ya kasance mazaunin nau'in agwagwar
ruwa da ake kira Penguins a turance.
Wakilin BBC yace an shafe sama da shekaru
goma ana gadin yankin da ke Antaktika, babu
wata kulawa da ake baiwa tekun da ya hada
kasashe da dama.
Tekun mai kankara shi ne mazaunin kashi uku na
agwagwar ruwan ko Penguean da ake da ita da
kuma tarin halittun ruwa.
Rasha dai ta dade ta na son ganin ba a cimma
yarjejeniyar ba, sai dai ministan harkokin wajen
New Zealand Murray McCully yace kasashe 24
da suka tattaunawar isun sa tabbatar da tsare
halittun tekun.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Antarctic: An cimma yarjejeniyar kare halittun ruwa"

Post a Comment