HUKUNCIN WANDA YA SABAWA AYOYIN RABON GADO*?
*Tambaya?*
Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke kokarin ganin an baiwa mace kason da aka bawa namiji wajen rabon gado?
*Amsa* :
Wa'alaykumussalam,
Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin hakan, saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar. Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya sabawa ayoyin rabon gado a cikin aya ta 14 a suratun Nisa'i. Wanda ya yi kira a daidaita namiji da mace a rabon gado saboda jahiltarsa da sharia ba za'a kafirta shi ba, Saboda ba duk Wanda ya aikata kafirci ba ne yake zama kafiri kamar yadda aya da hadisai da yawa suka tabbatar.
Allah ne mafi sani.
14/10/2016
*Amsawa*
*DR JAMILU ZAREWA*
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
0 Response to "HUKUNCIN WANDA YA SABAWA AYOYIN RABON GADO*? "
Post a Comment