Kananan yara ba su da makwanci a sansanin Calais da ke Faransa

Masu aikin agaji sun ce kusan yara 100 ba su
da makwanci mai kyau, amma kuma shugaban
gwamantin lardin ya ce yara 68 ne.
Fabienne Buccio ya ce wasu daga cikin mutanen
da suka saura a sansanin ba daga nan suke ba
tun asali.
Gwamnatin Faransa ta ce an kwashe kusan
mutum 5,600 zuwa cibiyoyin da za a ba su
kulawa tun ranar Litinin.
Wadanda aka kwashe sun hada da yara 1,500
wadanda ke zauna a cikin baca a sansanin kuma
ba tare da kowa ba.
Masu fafutuka sun ce a yanzu haka wurin ya
cika.
Sansanin dai ya zama wata babbar alama ta
rikicin 'yan gudun hijira a Turai inda mutanen da
ke zaune a cikinsa ke so su isa Ingila.
Masu aikin rusa sansanin dai na ci gaba da
kwashe ragowar tantuna daga yankin, wanda ya
lalace sakamako wuta da 'yan gudun hijirar da ke
barin wurin suka cinna masa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kananan yara ba su da makwanci a sansanin Calais da ke Faransa"

Post a Comment