Sojoji sun kashe mayakan IS '900' a Iraqi
kungiyar IS tsakanin 800 zuwa 900 tun lokacin
da dakarun Iraqi suka kaddamar da hare-hare
domin kwato birnin Mosul a makon jiya.
Joseph Votel ya shaida wa kamfanin dillancin
labarai na AFP zai yi wahala a san hakikanin
adadin mayakan IS din da aka kashe saboda
suna sajewa da fararen-hula.
An yi ittifakin cewa kawai mayakan IS 5,000 a
birnin na Mosul tun da aka fara kai musu
farmaki.
Tun daga lokacin, dakarun sojin Iraqi da na masu
fafutika, tare da tallafin sojojin Amurka sun
kwace garuruwa da dama daga hannun IS.
Manyan jami'an rundunar sojin kasar sun yi
gargadin cewa za a kwashe makonni ko ma
watanni da dama kafin a iya kwace birnin.
0 Response to "Sojoji sun kashe mayakan IS '900' a Iraqi"
Post a Comment