Matar farko da aka yi wa dashen fuska a duniya ta rasu

Matar da aka fara yi wa dashen fuska a duniya,
Isabelle Dinoire ta rasu, kamar yadda likitoci a
kasar Faransa suka bayyana shekaranjiya Laraba.
Sanawar da asibitin Amiens Hospital, wurin da
aka yi mata aikin dashen fuskar a watan
Nuwamban shekarar 2005, ya fitar, ta ce Isabelle
ta rasu ne ranar 22 ga watan Afrilun da ya
gabata, bayan doguwar jinya. Ta rasu tana da
shekara 49 a duniya, kamar yadda kafar labarai
ta CNN ta bayyana. Asibitin ya ce dalilin bayyana
labarin rasuwarta a makare, ya samo asali ne
daga wasiyyar da marigayiyar ta bari, wadda ta
bukaci kada a bayyana labarin rasuwarta ga
manema labarai.
Sai dai asibitin bai bayyana ciwon da ya yi
ajalinta ba. Kodayake, kafafen labaran kasar
Faransa sun ruwaito cewa rashin lafiyar da ya yi
ajalinta yana da nasaba da aikin dashen fuskar
da aka yi mata a baya.
An yi wa marigayiyar aikin dashen fuskar ne
lokacin da take da shekara 38 da haihuwa, bayan
karyarta ta cije ta a fuska. An dasa wa
marigayiyar wani bangare na fuskar wata mace
da ta kashe kanta ne.
Kuma shekara guda bayan aikin ne, Dinoire ta
ce: “Fuskar nan ba tawa ba ce, amma duk
lokacin da na dubi madubi, kaina nake gani.”
Aikin da aka yi wa marigayiyar a kasar Faransa
ya bude hanyar fara yin dashen wasu sassan
fuskar dan Adam a wasu kasashe shida, ciki har
da kasar Amurka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Matar farko da aka yi wa dashen fuska a duniya ta rasu"

Post a Comment