Fifa ta kirkiro kyautar karrama 'yan kwallo

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta kirkiro
sabuwar kyautar karrama 'yan wasan kwallon
kafa da suka yi fice, bayan da ta raba gari da
masu shirya kyautar Ballon d'Or.
Hukumar za ta sanar da wadanda za su lashe
kyautuka takwas da ta ware tsakanin maza da
mata masu taka leda da wadanda suke bayar da
gudunmawa a fagen tamaula a ranar 9 ga watan
Janairu a Zurich.
Fifa ta fara karrama 'yan wasa da jami'ai da
suka taka rawar gani a fagen tamaula a shekarar
1991 zuwa 2009 daga nan ne ta hada gwiwa da
mujallar Faransa mai gudanar da kyautar Ballon
d'Or.
A karkashin wannan sabon tsarin za a fitar da
zakarun bana ta hanyoyi biyu.
Hanyar farko kashi 50 cikin 100 zai kunshi
kuri'un kyaftin da kociyoyin tawagar kwallon kafa
da suke mambobi a hukumar kwallon kafa ta
duniya Fifa.
Haka kuma za a bai wa jama'a damar yin zabe
ta intanet da kuma manyan 'yan jarida 200 da
suke fadin duniyar nan.
A ranar Juma'a Fifa za ta bayyana 'yan wasa 23
da suke kan gaba a murza-leda, sannan ta ware
guda uku a ranar 2 ga watan Disamba, wadanda
daga cikinsu za a zabi zakaran bana.
Ga jerin kyautukan da za a lashe a shekarar
2016:
1. Dan wasan da ya fi yin fice
2. 'Yar wasan da ta fi yin fice
3. Mai horarwa da ya fi kowa iyawa
4. Wadda ta fi iya jan ragamar kwallon kafa ta
mata
5. Kwallon da aka ci mafi kayatarwa
6. Kyautar wasa ba da gaba ba
7. Kyautar magoya baya da suka fi da'a
8. 'Yan wasa 11 da babu kamarsu a cikin fili

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Fifa ta kirkiro kyautar karrama 'yan kwallo"

Post a Comment