An kashe dalibi yana kokarin sulhunta rikicin Naira 500

A ranar Litinin da misalin karfe 10 na dare ne
wani dalibi mai suna Aminu Badamasi da aka fi
sani da Justice mai kimanin shekara 28 da ke
sashin Ilimin Zamantakewa na Jami’ar Ahmadu
Bello da ke Zariya, ya rasa ransa a bayan da
wani matashi mai suna Yusuf Abdullahi da aka fi
sani da Mutuwa mai shekara 24 ya burma masa
wuka a ciki lokacin da yake kokarin sulhunta
wadansu kan bashin Naira 500.
Marigayin da wanda ake zargi da kashe shi suna
zaune ne a Layin Sule Ajasko da ke Jushi kusa
da Kwanar Maishanu a hanyar Jos a karamar
Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Yayan marigayin Balarabe Badamasi ya shaida
wa wakilinmu cewa, “Da misalin karfe 10 na dare
a ranar Litinin na fita domin in sa waya a caji sai
na ga marigayi kanena da abokansa su uku suna
hira sai muka gaisa na wuce. Na shiga shago ke
nan sai na ji hayaniya ina fita aka ce ai an kashe
Aminu kuma na hangi Yusuf Mutuwa rike da
wuka an rasa mai zuwa. A haka na yi kunar
bakin wake na fada masa na buge shi ya fadi
jama’a suka zo suka kama shi. Bayan tabbatar
da rasuwar kanina, sai matasa suka yi yunkurin
kashe Yusuf Mutuwa amma muka hana su har
’yan sanda su zo su kama shi, mu kuma muka
dauki gawar kanena muka kai gida shi ne aka yi
jana’izarsa.”
Mahaifiyar marigayin Malama Zainab Mohammed
cikin kuka ta ce danta ya samu kyakyawar
shaida domi a kan kokarin da yake yi wajen
sulhuntawa ne ake yi masa lakabi da Adalci
kuma a kan haka Allah Ya karbi rayuwarsa.
daya daga cikin abokan marigayin wanda abin ya
faru a idanunsa da ya nemi a sakaye sunansa, ya
ce, “Muna zaune sai muka ji ana jayayya
tsakanin Aminu Mai Indomi a kan raguwar bashin
kudin kwai Naira dari biyar da ya karba a hannun
Dini Abdullahi tun cikin azumi bai biya ba. Shi ne
shi marigayi Aminu ya taso domin ya sulhunta su
kuma ya cire Naira 500 ya biya Dini, sannan ya
yi musu nasiha. Shi Yusuf da ya yi kisa ba da shi
ake yi ba, kuma ba abin da ya shafe shi a
maganar. Kawai sai muka ga ya burma wa
marigayi Aminu wuka a ciki ya kuma yiwo kan
mutane.”
Wakilinmu ya ce bayan kammala jana’izar
marigayin matasa daga makabarta dauke da
makara sun wuce ofishin ’yan sanda suna cewa
sai ’yan sanda sun ba su Yusuf Mutuwa su
kashe shi tunda ya saba raunata mutane kuma
ya taba kashe wani a Abuja ya gudo ga shi
yanzu ya kara kisan kai, don haka a ba su shi su
kashe shi su huta. Sai da ’yan sanda suka yi
amfani da barkonon tsohuwa kafin su tarwatsa
matasan.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna,
ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar lamarin
inda ya yi kira ga jama’a su kwantar da
hankalinsu bayan sun kammala bincike za su
gabatar da wanda ake zargi a gaban shari’a
domin ya fuskanci hukunci.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kashe dalibi yana kokarin sulhunta rikicin Naira 500"

Post a Comment