Zaben Ondo: An yi zanga-zanga a Akure

Matasa sun fita kan tituna inda suka yi zanga-
zanga a birnin Akure na jihar Ondo, a Nigeria,
domin nuna rashin amince wa da dan takarar
jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar.
A ranar Alhamis ne hukumar zabe ta INEC ta
sanar da Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar
jam'iyyar, wacce ke mulkin jihar.
Shi dai Mista Ibrahim yana bangaren PDP ne da
ke biyayya ga Sanata Ali Modu Sheriff.
Hakan ba karamin koma-baya ba ne ga gwamnan
jihar Olusegun Mimiko, da kuma dan takar da ya
tsayar Eyitayo Jegedea, wadanda ke biyayya ga
bangaren Sanata Ahmed Makarfi.
A rana 26 ga wantan Nuwamba ne za a gudanar
da zaben.
Masu zanga zangar suna goyon bayan Eyitayo
Jegede, wanda ke cikin wani bangaren jam'iyyar
Makarfi. Ibrahim ya yi takara a karkashi
bangaren Ali Modu sheriff.
Jerin sunayen 'yan takarar gwamna da hukumar
INEC ta wallafa a ranar Alhamis, shi ne jerin
sunaye na karshe na 'yan takarar gwamna kuma
sun hada da 'yan takara 27.
Yayinda da ake kone-konen tayoyi da kuma toshe
hanyoyi a wasu wurare na birnin, kwamandan
'yan sanda ya bayar da tabbaci ga mazauna
Akure cewa ba sa tare da wani hadari.
Mai Magana da yawun 'yan sandar jihar, ASP
Femi Joseph, ya shaidawa kamfanin dillancin
labarai na Najeriya ce NAN cewa, 'yan sanda sun
jaddada anniyarsu ta kare lafiya da dukiyoyin
mutanen jihar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zaben Ondo: An yi zanga-zanga a Akure"

Post a Comment