Sudan ta Kudu: Kai Tap ya shafe kwanaki a boye cikin ruwa

Kai Tap, mai shekara 11 ya zauna shi kadai
yana muzurai, yayin da ya ke kallon sauran yara
suna wake-wake da wasanni a makarantar Eden,
wacce ke karkashin kariyar jami'an tsaron na
Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.
Bai dade da isa sansanin 'yan gudun hijrar da ke
garin Bentiu ba, da ke arewacin kasar, bayan ya
yi tafiyar kilomita 129 shi kadai cikin kwana hudu
daga Leer, inda fada ya kaure a 'yan kwanakin
baya.
Kai Tap ya ce fadace-fadacen ne suka ingiza shi
ya tsere daga sansaninsu ya bar 'yanuwansa a
can.
Ya ce, "Da dare ya yi sai su zo su yi ta harbin
mu, mu kuma sai duk mu watse."
"Muna gudu mu yi nutso a cikin ruwa domin
boyewa maharban," in ji Kai.
Kai Tap ya ce ba zai iya tuna wa ko kwanaki
nawa ya yi a cikin ruwan ba.
An sace garken shanun iyayensa, aka kuma
kashe dan'uwansa da ke kula da shanun, tare da
rusa gidansu.
Duk da ya samu mafaka, yana cikin damuwa
game da halin da 'yanuwansa ke ciki.
Kai ya kara da cewa, "Ban san halin da suke ciki
ba, ko suna raye ko sun mutu, saboda har yanzu
ana cigaba da fada."
"Hankali na ya rabu biyu, ina so in shiga
makaranta, amma kuma ina so in koma in dauko
iyayena."
Hauhawar farashin kayayyaki ya haura
kashi700%
Tsohon shugaban Botswana Festus Mogae,
wanda ke jagorantar hukumar da ke sa ido kan
yarjejniyar zaman lafiyar 2015, ya ce rikicin da
ke faruwa zai iya tayar da kurar wani rikicin da
ba za a iya kwantarwa ba.
Akwai rahotannin da ke cewa ana fada a Yei,
garin da ke kudu maso gabashi, da Leer da ke
arewaci da kuma Nasir da shi ma ke kudu maso
gabashin kasar.
A sakamakon tabarbarewar yanayin, ba a iya
daukar kaya ta hanya.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin
Duniya ya ce kara rincabewar rikicin na nufin
cewa dole su kara kai kaya da ma'aikata da
jami'an tsaro.
"Rashin abinci mai gina jiki a arewacin Bhr al-
Ghazal ya karu da ninki uku , don haka dole mu
kasance da ninki uku na kayan agaji don tinkarar
bukatun yara", Inji Mahimbo Mdoe, wakilin Unicef
a kasar.
Ya ce yanayin yayi kamari inda yara kusan
miliyan shida ne abun ya shafa.
Ya yi gargadin cewa muddun abubuwa ba su
sauya ba, yanayin zai iya ta'azzara ga fararen
hula, musamman mata da yara, kuma zai
kasance abu mai wuya ga ma'aikatan bayar da
agaji su kai gare su.
A cikin watan Agusta, kwamitin sulhun Majalisar
Dinkin Duniya, ya zartas da wani kuduri na
kirkirar rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen
yankin (RPF).
Ikon da aka ba ta ya hada da tabbatar da tsaron
Juba a matsayin wani wurin da fadan bai shafa
ba a gwagwarmayar neman iko tsakanin Shugaba
Salva Kiir da kuma Mataimakinsa da aka kora,
Riek Machar.
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta amince da a tura
rundunar, to amma tare da sharuda.
Kakakin Shugaba Kiir, Ateny Wek ya ce gwamnati
za ta tantance "daga inda dakarun suka fito da
kuma inda rundunar kariyar za ta kasance".
Idan har aka yi nasarar cimma yarjejeniyar, to
zai dauki watannin da dama kafin ta isa Sudan
Ta Kudu.
Yanzu dai Kai Tap na da damar zuwa makaranta,
amma sakon sa ga shugabannin kasar tasa da
ke cikin rudani shi ne, su tsayar da fadan hakan
nan.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sudan ta Kudu: Kai Tap ya shafe kwanaki a boye cikin ruwa"

Post a Comment