Kompany ya ce ya gaji da wasa — Guardiola

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya
nemi a sauya shi daga wasan da Manchester
United ta doke su da ci 1-0 idan an tafi hutun
rabin lokacin saboda ya "gaji."
Dan wasan, mai shekara 30, ya buga wasansa na
biyu a kakar wasa ta bana ne a karawar da suka
yi da United bayan ya yi jinya a watan Satumba.
Kocin City Pep Guardiola ya ce Kompany "ya
gaya mana cewa ya gaji, kuma ba zai iya buga
wasan ba bayan hutun rabin lokaci
City dai ba ta yi nasara ko sau daya ba a
wasanni shida da suka buga.
Guardiola ya kara da cewa abu mafi muhimmanci
a game da Kompany shi ne "bai ji rauni ba."
Kompany, wanda ke fama da ciwon sha-raba, ya
cew zai gaya wa likotoci gaskiya halin da yake
ciki na rashin lafiya.
Dan wasan na kasar Belgium ya buga wa City da
kasarsa wasa 25 a kakar wasan bara, wato ya
ragu daga wasa 38 a kakar wasan da ta gabaci
ta a bara da kuma ledar da ya murza sau 40 a
kasar wasa ta shekarar 2013-14.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kompany ya ce ya gaji da wasa — Guardiola"

Post a Comment