Ba’amurken kasar Sin ya kera jirgin da ke sauka a garejin gidansa

A Jihar Chicago ta kasar Amurka an samu
jama’a da injiniyoyi da suka mayar da bayan
gidansu filin jiragen sama, har ma suna ajiye
kananan jirage a garejinsu. Daga cikin wadannan
injiniyoyi akwai wani mutumin kasar Sin
zaunannen Amurka, mai suna Dabid Hu, wanda
injiniya ne da ke aiki a kamfanin kayan lantarki
na Nokia.
Wannan Ba’amurken dan kasar Sin ya fara kera
karamin jirgin sama ne tun a shekarar 2006.
Wato shekara 10 ke nan da ya fara wannan aiki
daga zane-zane a kwali, har ya fara sayen
sassan jirgin inda ya rika harhadawa. Dabid dai
ya hada jirginsa shi kadai, inda ya yi amfani da
lokutan da ba ya yin aikin komai.
Jirgin Dabid Hu yana da nauyin kilo 590, sannan
yana gudun kilomita 290 a kowace sa’a. Don
haka yana iya karade nisan kilomita 644 zuwa
724 a lokaci kankane.
Bayan da hukumar kula da jiragen sama ta
Amurka ta tantance ingancin jirgin, sai ya fara
tashi a cikin watan Yunin bana.
“Na sha tuka jiragen sama a tsawon rayuwata,
amma wannan shi ne karamin jirgi mafi inganci
da na taba tukawa. A tsarin sarrafa injinsa yana
da matukar nagarta ga dadin sauti,” a cewar
Musgrabe, wani jami’in bayar da horo a kamfanin
hada-hadar jiragen sama na Blue Sky Aero Inc.,
kamar yadda ya sanar da kamfanin Dillancin
Labarai na dinhua.
Ya ce karamin jirgin yana da “cikakkiyar kariya,”
inda ya kara da cewa, “komai a cikin jirgin yana
da cikakkiyar shaidar amincewata.”
Tun a watan Yunin bana aka fara hada-hadar
tashi da wannan jirgin saman, inda a halin yanzu
ya yi tafiye-tafiye na wata biyu, kuma ya shafe
sa’o’i 32, ta yadda aka kiyasta a kowane mako
yana cin dogon zango da yakan shafe akalla
sa’o’i biyu zuwa uku. Kuma babu wata matsala
da ta auku a gare shi.
“Wannan aiki ne da aka shafe shekara 10 ana
gudanar da shi. Iyalina sun fuskanci dimbin
kalubale wajen tallafa mini, inda suka fuskanci
damuwa da matsin rayuwa da rashin kudi.
Tamkar dai kowane gagarumin aiki, amma dai
farin cikina mun kai ga gaci,” a cewar Hu, bayan
da ya tashi da jirginsa a filin jirgin saman Morris
da ke bayan gidansa a ranar Lahadin da ta wuce.
“Na dai tashi sama a wannan jirgin. Don haka na
bude babin sabuwar rayuwa, inda kuma nake
hangen tunkarar wani al’amari nan gaba,” inji shi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ba’amurken kasar Sin ya kera jirgin da ke sauka a garejin gidansa"

Post a Comment