A ranar Asabar za a ci gaba da buga gasar La
Liga wasannin mako na 10. Sai dai Cristiano
Ronaldo na fama da rashin cin kwallaye a gasar
bana.
Dan wasan ya gamu da koma-baya ta fuskar cin
kwallaye tun lokacin da ya koma Madrid a
shekarar 2009, wanda ya ci guda hudu a bana
biyu a gasar La Liga
A tawagar kwallon kafa ta Portugal kuwa,
kwallaye biyar Ronaldo ya ci, hudu a karawa da
Andorra da daya a fafatawar da suka yi da
tsibirin Faroe a wasan neman shiga gasar cin
kofin duniya.
A kakar wasannin bara da aka kammala Luis
Suarez ne ya lashe kyautar wanda ya fi yawan
cin kwallye a gasar La Liga, inda ya ci 40; guda
30 Ronaldo ya ci a matsayi na biyu.
A kakar wasannin kwallon kafa ta bana Messi na
Barcelona ya zura kwallaye 14 a raga a wasanni
11 da ya yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

Related Posts :

  • Na fi so Ronaldo ya lashe Ballon d'Or — Zidane Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce Cristiano Ronaldo ne ya fi cancanta ya zama zakaran kwallom kafar duniya duk da cewa bai zu… ...
  • FA tana tuhumar David Moyes Hukumar kwallon kafar Ingila tana tuhumar kocin Sunderland David Moyes da zargin aikata ba daidai ba bayan an kore shi daga filin wasa rana… ...
  • Kompany zai ci gaba da murza leda a City -Guardiola Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce Vincent Kompany na da kyakkyawar makoma a kungiyar, amma yana bukatar sadaukawar domin ya rika … ...
  • A ranar Asabar za a ci gaba da buga gasar La Liga wasannin mako na 10. Sai dai Cristiano Ronaldo na fama da rashin cin kwallaye a gasar ban… ...
  • Ba za mu kori Rooney ba —Mourinho Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce babu inda kyaftin din kungiyar Wayne Rooney zai je. Mourinho ya yi watsi da rahotannin da ke … ...

0 Response to " "

Post a Comment