Ka san illar yin kudi dare daya?

Bayan kwashe fiye da shekaru 30 ta na aikin
kula da fasinjojin jirgin sama, Sandy Stein, mai
shekaru 65 a yanzu ta yi kudi.
Stein na da shekaru 53 lokacin da ta kirkiro wata
sarkar adana makullai wacce ake makalawa a
jikin jaka, ta yadda ba za'a sha wuyar laluben
makullai a cikin jaka ba.
A wannan shekarar ta sai mota mai tsada, ta
dauki mutane aiki kuma ta yi cinikin fiye da dala
miliyan hudu.
Wannan rayuwa ce mai dadi ga mutane da dama.
Sai dai kuma ga mamakin Stein, babban abinda
wannan arziki ya jawo mata shi ne kadaici.
Mijinta ya sake ta saboda a baya shi yake
daukar nauyin komai a gidan, don haka ya fara
kyashin arzikin da Stein ta samu. Alakarta da
kawayenta ma ta shiga tsaka-mai-wuya.
Tace "kawayena sun shiga hassada kuma sun
nuna min kyashi."
Kodayake mafi yawan mutane na ci gaba da
fatan yin kudi, masu kudin na cewa su na fama
da kadaici kuma rayuwarsu tafi ba da sha'awa ga
mai kallonsu daga nesa.
"Idan mutum ya yi kudin dare daya, tasirin hakan
na taba dukkan sassan rayuwarsa," in ji Dr.
Stephen Godlbart, daya daga cikin wadanda su
ka kafa kamfanin Money, Meaning & Choices
Institute, mai bai wa masu kudi shawarwari kan
yadda zasu tafiyar da rayuwarsu. "Ya kan jawo
tsananin bacin rai da takaici ga wasu mutanen."
Ya kara da cewa masu kudin dare daya kan samu
kansu cikin rudani tare da kadaici da bacin rai.
Namu ya samu
Da yawanmu mun shafe shekaru da dama muna
burin samun arziki. Amma da zarar kudin sun
samu sai mu gano cewa ba mu shiryawa sauye-
sauyen da zamu fuskanta daga mutanen da ke
kewaye da mu ba.
Da ma dai wannan ba wani batu ba ne da mu kan
bata lokutanmu mu na tunani a kai. Don haka
idan abokai su ka fara janye jiki (ko kuma su ka
kara matsarmu) sannan iyalanmu su ka fara
shiga harkokinmu wadanda ba su saba shiga ba a
baya, sai abin ya bamu mamaki.
A bangare guda, kudi kan sauya mutane. Wani
lokacin masu kudin dare daya, ku sun sani ko ba
su sani ba, kan sauya dabi'unsu ta hanyar
almubazzaranci ko daina wasu abubuwa da su
ke yi a baya, wadanda za su janyo musu rabuwa
da tsofaffin abokansu, in ji Megan Ford, shugabar
kungiyar masu bada shawara kan harkokin kudi
ta Amurka.
Ta kara da cewa "abokai ba zasu su so su sauya
kansu domin dacewa da sabon tsarin da ka zo
da shi ba", don haka sai su janye daga gare ka,
abinda zai kara maka takaici.
Samun kan 'yan uwa da abokan arziki shi ne yafi
wahalarwa. Mutanen nesa kan yi kokarin su biya
bukatar masu sabon kudi, amma 'yan uwa da
abokai su ne ke kokarin kara nanike wa wanda
su ke ganin yanzu ya zama gwarzo, in ji
Goldbart.
Kuma ya zaka yi idan 'yan uwa da abokai su ka
fara mai da kai wani dabam? Mafi yawanmu za
mu fara zargi ne. Ina wadannan 'yan uwan da
abokan lokacin da ka ke ta gwagwarmayar
neman arzikin? Hakan na sa kai ma ka ja jiki ka
takaita yawan abokanka, saboda ba ka tabbacin
waye ke kokarin kusantarka, kawai don 'ka shigo
gari'.
Wannan tunanin ba ya kaucewa idan kudin na ka
su ka zauna. Gano wanda ke neman abotar
gaske da kai na da matukar wahala kuma duk
lokacin da ka yi kuskuren amincewa da wani,
daga baya kuma ka gano cewa kudinka ya biyo,
sai ka kara gujewa mutane, a cewar Ford.
More arzikinka
Wadanda su ka yi kudin dare daya sun ce
sababbin damarmakin da su ke samu na kara
musu kadaici. Stephan Goss mai shekaru 28, dan
asalin Switzerland ne da ya koma San Diego ta
kasar Amurka da zama. Ya ce tilas ta sa shi
neman sababbin abokan da suke da irin damar
da yake da ita.
"Mafi yawan mutane ba zasu iya cewa bari mu
tafi Mexico hutu a gobe ba. Don haka sai ya
yawo da abokanka na da ya gagara saboda su ba
zasu iya barin wuraren ayyukansu ba," in ji Goss,
wanda ya kafa Zeeto Media, kamfanin da ya ke
bai wa masu wallafa a intanet damar sayar da
bayanansu.
Duk da yake Goss bai yi watsi da abokan da ya
yi lokacin tasowarsa a Switzerland da abokansa
na jami'a ba, a mafi yawan lokuta ya na rayuwa
ne tare da masu kudi 'yan uwansa da ke da
damar yin abubuwan da ya ke sha'awar yi.
Koda yake ita Stein ba ta ga haka, masana sun
ce tasirin kudin dare daya yafi sauki akan
tsofaffi, wadanda su ka jima su na aiki, saboda
makusantansu sun fi sa ran dama zasu samu
kudi, a cewar Goldbart.
Har Yanzu dai Stein ba ta daidaita sabanin da ta
samu da 'yan uwa da kawayenta ba. Sai dai
yanzu ta na da kyakkyawar alaka da manyan
ma'aikatanta guda biyar, wadanda tace ta gano
'yan amana ne.
Haka kuma yanzu ta fahimci kawayen da su ka
yi zaman gaskiya da ita lokacin da ta ke aikin
jirgin sama kuma ta na yi musu kyauta sosai.
Daga cikin abinda yafi mata dadi shi ne daukar
wata abokiyar aikinta da ta yi zuwa yawon kallon
dabbar 'bear' din da ke rayuwa cikin kankara.
Ta ce; "Na yi matukar farin ciki da na samu
damar yin haka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ka san illar yin kudi dare daya?"

Post a Comment