'Mutum na gab da karar da halittun duniya'

Wani rahoto mai tayar da hankali na hadin guiwa
da kungiyar kare halittu da muhalli ta WWF, da ta
kare dabbobi ta Zoological Society ta Landan ya
nuna cewa dan-adam ya karar da kashi 60 cikin
dari na dabbobi masu kashin baya a duniya tun
daga 1970.
Rahoton ya yi gargadin cewa idan lamarin ya ci
gaba da kasancewa haka za a wayi gari an
kawar da tsarin cude-ni-in-cude ka da halittun
duniya gaba daya suka dogara a kansa ya gushe.
Masu binciken da suka hada rahoton sun yi
nazarin bayanai kan kusan nau'in dabbobi ko
halittu daban-daban har 4000.
Rahoton ya gano cewa sha'awa ko marmarin
dan-adam, halittar da yawanta ya linka biyu a
shekara 50 da ta wuce, yana cinyewa da
cunkushewa da kuma gurbata abokan zamansa
na duniya har su kare.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Mutum na gab da karar da halittun duniya'"

Post a Comment