Zan ci gaba da fitowa a fina-finai - Ibrahim Mandawari

An nada babban mai ruwa da tsaki a harkar fina-
finan Hausa ta Kannywood, Ibrahim Muhammad
Mandawari, a matsayin mai unguwar Mandawari,
da ke cikin birnin Kano.
A ranar 7 ga watan Oktoba ne dai aka tabbatar
da nadin a gaban hakimin Dala, sannan kuma mai
martaba Sarkin Kano, Muhammad Sunusi na biyu
ya amince da nadin.
Ya gaji mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Auwalu
Shawai, wanda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi
na daya ya nada, a zamaninsa.
Ibrahim Mandawari dai na daga cikin mutanen da
suka assasa harkar fina-finan Hausa ta zamani a
da ake kira Kannywood.
Ya shedawa BBC cewa zai ci gaba da shiryawa
da kuma fitowa a fina-finan Hausa irin wadanda
ya saba fitowa a baya.
'Yan uwa da abokan arziki dai sun taya shi
murna bisa wannan nadin na sa

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zan ci gaba da fitowa a fina-finai - Ibrahim Mandawari"

Post a Comment