Buhari zai kashe $10bn a Naija Delta

Gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari za ta kashe $10bn a yankin Naija Delta
da zummar kawo karshen hare-haren masu tayar
da kayar-baya.
Minista a ma'aikatar man fetur Emmanuel Ibe
Kachikwu, wanda ya bayyana hakan, ya kara da
cewa za a yi amfani da kudin ne domin gina
hanyoyin mota da na jirgin kasa da
makamantansu.
Wannan batu dai na zuwa ne a daidai lokacin da
masu tayar da kayar-baya na yankin ke ci gaba
da fasa bututan mai, lamarin da ya sa kasar ta yi
asarar biliyoyin naira.
Mr Kachikwu ya ce Shugaba Buhari zai gana da
masu tayar da kayar-bayan da masu rike da
sarautun gargajiya na yankin a makon gobe.
Su dai masu tayar da kayar-bayan suna so ne
gwamnati ta kashe kudade da dama a yankin
domin rage radadin talaucin da ke addabarsu.
Masu sharhi dai na dora laifin talaucin da yankin
ke fama da shi a kan 'yan siyasar yankin,
wadanda suka gaza inganta rayuwar talakawa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari zai kashe $10bn a Naija Delta"

Post a Comment