An kai hari a sansanin sojin Amurka na Afghanistan

Karar fashewar wasu manya-manyan bama-bamai a sansanin sojin Amurka da ke Bagram a Afghanistan ta yi sanadin mutuwar akalla mutum hudu.
Wani dagaci a yankin, Haji Shookor, ya shaida wa BBC cewa akalla mutum 14 ne kuma suka samu raunuka sakamakon fashewar bama-baman.
Kungiyar Taliban ta ce wani dan kunar-bakin-wakenta ne ya kai harin, wanda rahotannin ke cewa ya lalata dakin girkin sansanin.
Ana kallon harin a matsayin wata gazawar jami'an tsaro musamman ganin yadda yankin ke da matukar tsaro.
Ana amfani da Bagram, wanda ke arewacin Kabul babban birnin kasar, a matsayin sansanin sojin kasa da na sama na dakarun da Amurka ke jagoranta da kuma kungiyar tsaro ta Nato fiye da shekara 14.
An ambato wani jami'in gwamnati a yankin na cewa maharin ya shiga sansanin ne da sassafe ba tare da abin hawa ba, inda ya saje da ma'aikata.
Abdul Wahid Sediqi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "Ba mu san wanda ya kai harin ba, amma yana cikin leburori 'yan kasar Afghanistan da ke aiki a sansanin."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kai hari a sansanin sojin Amurka na Afghanistan"

Post a Comment