An kama dalibi dan Nigeria da kwayoyi a Mauritius

An kama wani dalibi dan Najeriya a kasar
Mauritius bayan an kwace wani abu wanda ake
zaton kwayoyi ne da ya kunshe a wasu kananan
robobi.
A ranar Talata ne dai 'yan sanda suka kama
Uchenna Philips Okafor mai shekara 23 a garin
Flic-en-Flac da ke bakin ruwa a lokacin da suke
aiki a boye na neman masu laifi.
Har yanzu Mista Okafor, wanda ke zaune a
tsibirin Mauritius bai mayar da martani a kan
zargin da ake mai na hulda da miyagun kwayoyi
ba.
Mista Okafor ya zuba kwayar heroin mai nauyin
giram 25 wanda kuma darajarta ta kai dala
103,000 a cikin kananan robobin man shafawa
guda 26.
'Yan sanda sun ce hukumar kula da shige da fice
da jami'an da ke kula da harkokin miyagun
kwayoyi sun dakatar da shi a filin jirgin sama na
tsibirin a ranar Lahadi.
An aike wa Mista Okafor sakon ne daga filin
jirgin saman Charles de Gaulle da ke kasar
Faransa.
'Yan sanda sun ce an kwace kudin Mauritius da
na kasar Bangladesh da takardar shaidar zama
dan kasa ta bogi na Mauritous daga hannun
Okafor.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kama dalibi dan Nigeria da kwayoyi a Mauritius"

Post a Comment