An zabi wani musulmi bakar fata kansila a Amurka

An zabi wani musulmi bahaushe dan asalin
kasar Ghana a matsayin kansila a Majalisar
Karamar Hukumar birnin Portland Maine da ke
jihar Maine ta Amurka.
Zaben nasa na zuwa ne yayinda Musulmi da
sauran baki a Amurkar ke ci gaba da nuna
fargaba game da makomarsu a kasar bayan
zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasa;
saboda matakan da ya ce zai dauka na ko dai
kora, ko na hana wasu shiga kasar.
A cikin wata hira da sashen Hausa na BBC
sabon kansilan Pious Ali ya ce aikin da ya yi na
baya a hukumar ilmi ta karamar hukumar ne ya
taimaka wajen zabensa.
'' (An zabe ni ne) domin mutane sun ga aikin da
nake yi. Sun ga aiki na aiki ne na taimakon yara.
Shi ya sa kowa na son mai taimakon yara.''

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An zabi wani musulmi bakar fata kansila a Amurka"

Post a Comment