Ko me ya sa mutane ke jima'i da 'yar tsana?

Wani Fim mai taken 'Westworld' wato yammacin
Turai, ya nemi sani dangane da irin yadda
rayuwar jima'i za ta kasance a nan gaba
musamman bisa la'akari da yadda fasahar
kimiyya take kara bunkasa a kullum. Hakan ne
ma ya sanya Brandon Ambrosino ya rubuta
wannan kasida.
Misali ace kai attajiri ne wanda zai iya kashe
tsabar kudi har $40,000 domin ya ziyarci garin
da babu doka da oda, rana daya. Ka ga ke nan
za ka iya aikata duk irin ta'asar da kake son
aikatawa.
Za ka iya yin kisan kai. Za ka iya yin fyade.
Sannan za ka iya huce haushinka a kan duk
mutumin da ka ga dama. Koma me ka yi a irin
wannan gari, babu laifi domin babu doka da oda
a cikinsa.
Saboda haka, kusan za a iya cewa mutane
kalilan ne kawai za su iya sanin irin abin da ka
aikata a wannan garin kuma watakila ma su
nemi su karfafa maka gwiwa wajen cigaba da
aikata hakan.
Da alama al'amarin ya munana ko?
To amma misali idan aka ce wannan garin da
muke batu akai da kuma duk irin ta'asar da aka
yi, gari ne da ya kunshi 'yar tsanar Mutum-
mutumin da aka kera da halayya irin ta dan
adam domin kawai ta biya maka bukata, shin ko
hakan ya kai munin misalin da muka bayar na
farko?
Su dai mutum-mutumi komai yawansu ba za su
cutar da dan adam ba. Yanzu haka dai wannan
batu ne yake cin kasuwa a fim din 'westworld'.
Shi dai wannan fim ya mayar da hankali ne a kan
rayuwa a wurin shakatawa wanda ke cike da 'yar
tsanar ta Mutum-mutumi, a inda mutane ko
kuma masu yawon bude ido suke yin duk abin da
suke so da su.
Wani kwararre mai kirkirar Mutum-mutumi da ake
kira Jeffrey Wright ya ce " An kirkiri 'yar tsanar
ne domin gamsar da mutanen da suka ziyarce su
da kuma biya musu duk wata bukata da suke da
ita."
Yin Jima'i ta Intanet
"A koyaushe mutane suna biyan kudi domin yin
jima'i." In ji Maeve Millay, wata magajiyar gidan
karuwai a fim din na 'westworld', yayin da take
magana a kan halayyarsu ta 'yar tsana.
Ta ci gaba da cewa "banbancin kawai shi ne ana
kididdige kudin da za a ba mu idan aka sadu da
mu kuma a biya nan take."
Abin da Maeve take son nunawa shi ne dole ne
ka biya duk wata mace da ka sadu da ita.
Ita dai Maeve, wata 'yar tsana ce wanda aka
kirkire ta domin ta biya wa duk mutumin da ya
ziyarci wannan wurin shakatawar bukata ta
jima'i.
Tana kuma jan hankalin mutanen da su ba su da
niyyar saduwa da 'yar tsana sakamakon mallakar
mata a gidajensu.
Ko akwai Banbancin tsakanin Mace da 'yar
tsanar?
Bisa tsari halittar da aka yi wa 'yar tsanar mai
kama da mutum, tana da farji da ke yin duk irin
abin da na 'ya mace yake yi. Suna sumbartar
masu saduwa da su. Suna yin kukan dadin
jima'i. Sannan kuma suna nuna gamsuwa ko
rashin gamsuwa da jima'i.
To amma wasu masu sukar wannan al'amari,
suna ganin fim din na 'westworld' yana kokarin
bayyana cin zarafin mata ta hanyar jima'i.
Suna ganin cewa irin yadda aka ci zarafin 'yar
tsanar da aka yi wa lakabi da Dolores a wasan
kwaikwayon wadda kuma ta fara kokarin tuna
abin da maza suka yi mata a baya, hanya ce ta
cin zarafi ta hanyar jima'i.
A zahiri, duk wata 'yar tsanar da aka kirkira mai
halittun mata a fim din na 'westworld', to an yi ta
ne domin biyan bukatar maza.
To sai dai abin tambaya a nan shi ne shin ko ana
neman amincewarsu kafin saduwa da su?
Baya ga saduwa da irin wannan 'yar tsanar,
akwai abubuwa da dama da ake yi musu
wadanda alal-hakika ba za a iya yi wa dan adam
ba, kamar kisan su da ake yi.
Koma dai wace irin azabtarwa ake yi wa
wadannan irin 'yar tsanar ko kuma Mutum-
mutumi, a kowane dare, masu kula da wurin
shakatawar suna goge komi daga kwakwalwarsu.
Ana kuma yin hakan ne bisa tunanin cewa abin
da ya sanya sabawa dan adam yake da muni shi
ne yadda dan adam din yake iya tuna duk abin
da aka yi masa.
Babu shakka, abubuwan da wannan wasan
kwaikwayon yake kokarin neman sani a kai, ba
abin da za a ki mayar da hankali a kai ba ne
domin ba wai kawai al'marin ya shafi duniyar
kimiyyar fasaha ba ne.
Wannan ne ya sanya wata masanin halayyar dan
adam, Sherry Turkle wadda ta yi bincike kan
alakar dan adam da kimiyyar fasaha, fadin cewa
bai kamata tunaninmu kan yadda kimiyyar fasaha
za ta kasance a nan gaba ba ya takaita ga
rayuwar 'yar tsananar Mutum-mutumi ba.
Ta kara a cewa kamata ya yi a mayar da hankali
kan irin mutanen da za mu zama a nan gaba.
Misali masu kallon fina-finan batsa ne? Ko kuma
masu yawan son biya wa abokan zamansu
bukatunsu na jima'i ne?
To amma Ford wani mai bincike kan abin da ya
sanya mutane azabtar da Mutum-mutumi, ya yi
ikrarin fahimtar dalilin da ya sa mutanen suke
son kashe mukudan kudi wajen kashe da yin
jima'i da 'yar tsanar, wato saboda ba mutum ba
ce.
Idan kana son karanta wannan labari da harshen
Turanci, sai ka latsa wannan Would sex with a
robot be infidelity

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ko me ya sa mutane ke jima'i da 'yar tsana?"

Post a Comment