Chelsea ta karbe ragamar Premier

Chelsea ta karbe jagorancin teburin Premier
bayan da ta bi Middlesbrough har gida ta doke
ta da ci 1-0, a wasan mako na 12 na gasar ta
Premier.
Diego Costa ne ya ci wa Chelsea kwallon a minti
na 41 da wasa, kuma dan wasan ya kasance jigo
wajen kai hare-hare a wasan a bangaren
Chelsea.
Wannan shi ne karo na farko da Middlesbrough
ta yi rashin nasara a cikin wasanni hudu da ta
yi.
Yanzu Chelsea ta tsallako da maki 28 ta wuce
Liverpool wadda kafin wasan ita ce ta daya, da
kuma Manchester City ta biyu, masu maki 27
kowacce, yayin da Boro take ta 15 da maki 11,
mataki daya tsakaninta da faduwa daga tebur.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Chelsea ta karbe ragamar Premier"

Post a Comment