Kiristoci a arewacin Najeriya sun yabawa Buhari

Onarebul Keften Amuga wailin Tangale
wanda ya jagoranci kungiyar kiristocin
arewa a taron manema labarai yace dole ne
su fito su nuna goyon bayansu ga shugaba
Buhari.
– A cewar Keften Amuga shekaru hamsin da
shida ke nan kiristocin arewa ke taka rawa a
fannin siyasar kasar ba tare da sanin inda
suka dosa ba amma yanzu canji ya zo.
A lokacin kemfen shugaba Buhari yace
muddin korostocin arewa suka zabeshi zai
nada kirista daga arewa ya zama sakataren
gwamnati tarayya. Alkawarin da yayi ke nan,
inji Kefene Amuga.
Ku Karanta: Daruruwan yan Boko Haram na
cigaba da mika wuya
Yace Shugaba Muhamad Buhari ya cika
alkawarin da yayi inda ya nada Injiniya David
Lawal Babachir a matsayin sakataren
gwamnatin tarayya, matsayin da babu wani
kiristan arewa ya taba samu. Baicin Babachir
Onarebul Yakubu Dogara ya zama kakakin
majalisar wakilai ba tare da tsangwama ba
daga shugaban kasa kamar yadda aka saba
gani can baya.
A cewar wakilin Tangale lailai Shugaba
Muhammad Buhari yana son ‘yan arewa su
zama daya, wato da kirista da muslmi ‘yan
arewa su zama daya. Yace ba maganar baki
ba ce kawai. Sun ga Buhari ya aiwatar da
wannan a mulkinsa.
A nashi jawabi mai baiwa shugaba Buhari
shawara a harkar siyasa kuma dan kungiyar
kiristocin arewa Ayuba Musa Birma yace
wani abu mai mahimmanci a mulkin Buhari
shi ne shawo kan rikicin ta’adanci da ya
addabi arewa maso gabas. Yace canji ya
kawo zaman lafiya. Yace shi kansa dan
gudun hijira ne da rikicin Boko Haram ya
daidaita amma da zuwan gwamnatin Buhari
ya koma garinsu da iyalansa.
Sun yiwa shugaba Buhari fatan Allah ya
bashi tsawon rai da koshin lafiya. Baicin
haka kiristocin arewa suna bayan shugaban
dari bisa dari.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kiristoci a arewacin Najeriya sun yabawa Buhari"

Post a Comment