Jami'an kasar Turkiyya na neman mafaka

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO ya ce
jami'an kasar Turkiyya da dama, wadanda aka
tura kungiyar tsaro ta Nato na neman mafaka
tun lokacin da ba su samu nasara a yunkurin
juyin mulkin kasar ba.
Jen Stoltenberg ya ce jami'an sun nemi mafaka a
kasashen da aka tura su amma kuma ba su
bayyana sunayensu da adadi da kuma dalilin
bukatar tasu ba.
Kasashen da abin ya shafa za su duba lamarin.
Turkiyya dai ta sallama, tare da kora, da tsare ko
kuma daure dubban mutane tun yunkurin juyin
mulki da aka yi watan Yuli.
Da damansu sun yi aikin Soja, duk da dai cewa
wasunsu malamai ne da 'yan sanda da alkalai da
kuma 'yan jarida.
Gwamnatin Turkiyya na kai hari ne kan wadanda
take zaton suna da alaka da Fethullah Gulen,
mutumin da suka yi amannar ya jagoranci
yunkurin juyin mulkin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jami'an kasar Turkiyya na neman mafaka"

Post a Comment