Gwamna zai nada makaho mataimakin sa

Jiya ce ranar da Majalisar Dikin Duniya ta
kebe domin fadakar da al’umma ma’anar
farar sanda da makaho ke rikewa da kuma
abun da ake bukata daga masu gani da
idanunsu lamarin da ya sa gwamnan jihar
Bauchi ya sha alwashin warware matasalolin
makafin jihar.
Kamar yadda aka bayyana mai rike da
sandar yana bukatar taimako na musamman
ne daga kowane mutum ya hadu dashi.
Governor Muhammad Abdullahi Abubakar of
Bauchi state
Idan an gansu suna rike da farar sanda to
kamata yayi a tsaya su wuce. Idan kuma ta
kama a taimakesu ketare hanya ko kaucewa
wani wurin da zai kawo masu wani hadari ko
cikas sai a taimaka masu.
Ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe
rana ce da makafi kan mika sakonni ga
gwamnatoci dangane da irin halin da suke
ciki, tare da bayyana matasalolin da suke
fuskanta.
Malam Iliya Adamu mai kula da harkokin da
suka shafi makafi a shiyar arewa maso
gabas ya bayyana irin kokensu musamman
su da suka fito daga yankin arewa maso
gabas. Yace mafi yawa akan yi magana akan
masu gudun hijira amma basa magana akan
makasassu musamman ma makafi.
Yakamata a san akwai makafi da gudun
hijira ya samesu, inji Adamu.
Idan makafi sun samu kansu cikin gudun
hijira ba’a kula dasu balantana ma a damu
dasu, a cewar Adamu. Ya bukaci a sasu
cikin hukumar da ake kokarin kafawa akan
nakasassu.
Su ma wasu makafin sun fadi albarkacin
bakinsu. Shugaban matasan makafi na
arewa maso gabas yace babban matsalarsu
ita ce rashin kulawa daga shugabanninsu da
gwamnatoci. Misali yace sun goyi bayan
barace barace maimakon bada taimakon da
zai sa su yi dogaro da kansu. Yakamata a sa
yara kanana a makaranta domin a basu ilimin
da ya cancanta dasu.
Wata makauniya tace sai ta fita tayi bara
kafin ta samu abun da zata ci ta sha, ta sayi
sabulun wanki ko na wanka.
A jawabin da gwamnan jihar Bauchi Barrister
M.A. Abubakar yayi ya ba makafin tabbacin
duba koke-koken da suka gabatar masa.
Yace ranar farin ciki ce gareshi. Dangane da
koke-koke guda takwas da suka ba gwamnan
yace zai zauna da shugabanninsu zasu yi
shawara. Ya nemi su bashi mutum guda da
zai nada mataimakinsa akan harkokin
makafi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gwamna zai nada makaho mataimakin sa"

Post a Comment