Fidel Castro babban mai kama-karya ne— Trump

Sabon zababben shugaban Amurka Donald
Trump ya bayyana Fidel Castro, tsohon
shugaban Cuba da ya rasu, a matsayin mai
kama karya da ya kuntata wa mutanen kasar
shi.
Mista Donald Trump ya ce abin da za a tuna
Fidel Castro da shi, shi ne, kuntatawa da talauci
da take hakkokin mutane.
Lokacin da yake yakin neman zabe, Mista Trump
ya yi barazanar lalata kyakyyawar alaka da
Amurka ta sake kullawa kwanannan da Cuba.
Tunda farko, shugaba Obama na Amurkan ya ce
ya so kulla zumunci da mutanen Cuba, inda ya
ce gwamnatin shi ta yi aiki tukuru don dinke
barakar dake tsakanin kasashen biyu.
Shugabannin kasashen duniya da dama na ci
gaba da jimamin mutuwar tsohon shugaban
kasar Cuba, wanda ya kangare wa Amurka a
lokacin yakin cacar baka, Fidel Castro.
Shugaban China Xi Jinping ya ce 'yan kasar
China sun yi rashin babban aboki, yayin da
shugaba Putin na Rasha ya bayyana shi a
matsayin tauraron wani zamani.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ma ya ce
ya yi bakin ciki da jin labarin mutuwar tsohon
shugaban, dan juyin juya-hali, wanda yafi
kowanne dadewa yana shugabancin Cuba.
Cikin wata sanarwa, shugaba Buhari ya bayyana
Fidel Castro a matsayin zakakurin shugaba
wanda ya bunkasa fannonin ilimi da kiwon lafiya
da wasanni, da har wasu kasashen duniya ke cin
moriyarsu.
Ya kuma bayyana shi a matsayin babban abokin
nahiyar Afirka, wanda ya bayar da gagarumar
gudun muwa wajen neman 'yan cin kasashen
nahiyar.
A wata hira da BBC, fitaccen mai sharhi kan
harkokin yau da kullun a Najeriya, Mahmud Jega,
ya ce marigayi Fidel Castro ne mutumin da ya fi
kowanne bai wa nahiyar Afirka taimako na
samun 'yanci:
Shi ma Paparoma Francis ya bayyana mutuwar
Fidel Castro a matsayin wani abin bakin ciki,
sannan ya yi mushi addu'o'i.
Shugaba Jocob Zuma na Afirka ta Kudu ma ya
bayyana marigayin a matsayin mutumin da ya yi
tsayuwar daka don tabbatar da 'yan cin wadanda
ake dannewa a fadin duniya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Fidel Castro babban mai kama-karya ne— Trump"

Post a Comment