Majalisar dinkin duniya ta zargi Burma da kisan Musulmi

Wani babban jami'ai na majalisar dinkin duniya
ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Myanmar ko
Burma tana yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya
tsiraru kisan kare-dangi.
Dakarun sojin kasar dai sun yi ta kisan 'yan
kabilar ta Rohingya a jihar Rakhine, lamarin da ya
tilasta musu tserewa zuwa makwabciyar kasar
Bangladesh, in ji John McKissick, na hukumar
kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin
duniya.
Gwamnatin kasar dai ta kaddamar da hare-haren
da ta ce na kawar da masu tayar da kayar baya
ne da ke kai hare-hare a kan iyakarta tun watan
Oktoba.
Ta musanta zargin da babban jami'n majalisar
dinkin duniyar ya yi.
Jami'an gwamnatin sun ce 'yan kabilar ta
Rohingya suna banka wuta kan gidajensu a jihar
ta Rakhine domin su dora alhakin hakan kan
gwamnati.
BBC ba za ta iya zuwa yankin domin tantance
gaskiyar al'amari ba saboda an hana 'yan jarida
da masu bayar da agaji shiga yankunan.
'Yan kasar ta Myanmar 'yan kabilar Buddha
mafiya rinjaye suna yi wa Musulmi 'yan kabilar
Rohingya, wadanda suka kai miliyan daya, kallo a
matsayin bakin-haure da suka shiga kasar daga
Bangladesh.
'Gaba kura baya sayaki'
Duk da yake dokokin Bangladesh ba su bai wa
bakin-haure damar shiga kasar ba, amma
ma'aikatar harkokin waje ta ce dubban 'yan
kabilar ta Rohingya sun nemi mafaka a kasar.
Rahotanni sun ce dubban 'yan kabilar ta
Rohingya na can suna taruwa a kan iyakar kasar.
Mr McKissick ya ce dole ne a fara duk wani
yunkuri na magance matsalar kan "dalilan da
suka kawo ta."
Ya kara da cewa sojojin Myanmar da jami'an da
ke kula da kan iyakar kasar sun hada gwiwa
wajen gallazawa Musulmin na kabilar Rohingya
bayan an kashe jami'an da ke kula da iyaka tara
a farkon watan Oktoba, lamarin da wasu ke dora
alhakinsa kan masu tayar da kayar baya na
Rohingya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Majalisar dinkin duniya ta zargi Burma da kisan Musulmi"

Post a Comment