FA ta kara cin tarar Mourinho bisa kalamansa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sake cin tarar
Jose Mourinho, saboda kalaman da ya yi kan
alkalin wasa Anthony Taylor, inda ta ce kalaman
kocin sun nuna duk yadda lafirin ya yi ba zai
tsira ba.
Taylor shi ne ya hura karawar da Liverpool da
Manchester United suka tashi canjaras a gasar
Premier da suka yi a Anfield a watan jiya.
Hukumar ta ce Mourinho ya biya tarar fam
50,000 kan kalaman da ya yi cewar zabo alkalin
wasa Taylor ya saka matsi kan jami'an
Manchester United.
A ranar Laraba hukumar ta ce kalaman nasa na
nufin ta kowanne fanni alkalin wasan na tsaka
mai wuya, ko ya taka rawar gani ko kuma bai yi
ba.
Bayan tarar da hukumar ta ci Mourinho ta kuma
gargade shi da ya guji sake jefa kansa cikin irin
wannan lamari wanda ya yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "FA ta kara cin tarar Mourinho bisa kalamansa"

Post a Comment