Sojojin Nigeria sun caccaki Amnesty International

Rundunar sojin Najeriya ta ce zargin da kungiyar
kare hakkin dan adam ta Amnesty International
ta yi mata na kisan mutum 150 tsakanin watan
Agustan shekarar 2015 zuwa Agustan shekarar
2016 ba gaskiya ba ne.
A wata hira da kakakin rundunar sojin kasa
Kanar Sani Usman Kukasheka ya yi da BBC
bayan sanarwar da suka fitar kan batun, ya ce
Amnesty International ta saba yin karya kan
sojojin Najeriya.
Ita dai kungiyar Amnesty International ta ce
mutanen da aka kashe 'yan fafutikar ganin an
kafa kasar Biafra ne.
Sai dai Kanar Kukasheka ya ce masu fafutikar
sun kashe mutane da dama - wadanda ba 'yan
kabilarsu ba ne - a yankin kudu maso gabashin
kasar a yunkurin da suke yi na tayar da zaune
tsaye.
A cewarsa, "Tabbas wasu kungiyoyin da ba sa
son zaman lafiya sun aikata kashe-kashe
tsakanin watan Agustan shekarar 2015 zuwa
watan Agustan shekarar 2016 a kudu maso
gabashin Najeriya".
Ya kara da cewa "sun karkashe mutanen da suka
fito daga wasu sassan kasar nan, suka kona su.
Irin wadannan kashe-kashe ka iya jawo rikicin
addini da yin barazana ga tsaron kasa shi ya sa
rundunar soji ta tsoma baki."
'Ba sa son zaman lafiya'
Kanar kukasheka ya kara da cewa 'yan kungiyar
MASSOB/IPOB da suka yi zanga-zanga a watan
Mayun shekarar 2016 sun kashe 'yan sanda biyar
kana suka jikkata wasu sojoji, baya ga banka
wuta kan motocinsu.
Kazalika, a cewarsa, sun yin arangama da sojoji
abin da ya sa wasu sojojin suka samu munanan
raunuka, amma kungoyoyi iri su Amnesty ba su
ce komai ba.
Kakakin rundunar sojin ta Najeriya ya ce
Amnesty International da kungiyoyi irin ta na so
a tayar da rikici a kasar shi ya sa suke sanya
baki a aikin wanzar da zaman lafiya da sojoji ke
yi.
Ya yi kira ga 'yan kasar da su daina yarda da
abubuwan da kungiyoyi kamar Amnesty
International ke fada a kan su, yana mai cewa
suna yin wadannan maganganu ne domin a ce
suna yin aikinsu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sojojin Nigeria sun caccaki Amnesty International"

Post a Comment