Tanzania: Likitoci sun gagara yi wa Elias aiki

Wani mutum dan asalin kasar Tanzani, ya
shaidawa BBC cewa asibitin da ya ke ziyarta sun
gagara yi masa aikin tiyata saboda tsahonsa.
Baraka Elias, mai tsaho kafa bakwai da inci
hudu, ya ce ya na da lalura a kwankwasonsa
saboda raunin da ya ji a lokacin da ya fadi, kuma
ana bukatar ayi masa aikin gaggawa.
Likitocin da suke kula da lafiyar Mista Elias a
babban asibitin kashi na gwamnati da ke Dar as-
Salam, sun shaida masa cewa, tsahon da ya ke
da shi ba zai bari ya kwanta salin-alin ba a
gadon asibitin.
Haka kuma likitocin asibitin Muhimbili sun ce
injin da ke daukar hoton jikin dan adam dan
binciken kwakwaf ba a yi shi dan mutane dogaye
kamar Mista Elias ba.
Labarin Mista Elias da ya fi kowa tsaho a baki
dayan kasar Tanzania ya karade kafofin yada
labaran kasar, inda mutane ke tururuwa dan
ganewa idanun su.
Kowanne mutum ya zo babu abinda ya ke fata
face ya tsaya kusa da Mista Elias inda za ka ga
mutum ya yi dan kankani a gaban sa, wasu
hotunan Internet da aka wallafa ya nuna yadda
mutanen ke tsaye a kusa da shi.
Ya kara da cewa shi ya na mamakin yadda
mutane ke al-ajabin tsahon shi, amma shi sam
baya jin wani banbanci tsakanin sa da sauran
mutane, kuma ya na gudanar da harkokin sa na
yau da kullum kamar yadda kowanne dan adam
ke yi.
Kasar Tanzania dai na daga cikin kasashe a
nahiyar Afurka da bangaren kiwon lafiya ke cikin
mawuyacin hali, tun daga kan kwararrun likitoci,
har zuwa kan rashin kayan aiki.
To Amma likitoci sun tabbatar da cewa za a iya
yi wa mista Elias aiki amma sai an dangana da
kasashen turai.
Iyayen Mista Elias dai sun tabbatarwa da
kamfanin dillancin labaran kasar cewa, tsahon na
shi na gado ne.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Tanzania: Likitoci sun gagara yi wa Elias aiki"

Post a Comment