An sace tsohon Minista a Najeriya

A Najeriya, wasu 'yan bindiga wadanda ba a
tantance ko su wanene ba, sun sace wani
tsohon ministan kasar, Ambassada Bagudu
Hirse, lokacin wani hari a gidan shi dake
Kaduna.
Rahotanni na cewa 'yan bindigar sun kai hari a
gidan ne da yammacin Lahadi, inda suka yi
musayar wuta da masu gadin gidan.
Rundunar 'yan sandan jahar Kaduna ta tabbatar
da lamarin.
Kakakin rundunar, ASP Aliyu Usman ya ce duk da
cewa ba a kama ko daya daga maharan ba,
jami'an 'yan sanda sun baza komar su domin
gano wadanda suka sace tsohon ministan.
Sace sacen jama'a don neman kudin fansa dai
na ci gaba da zama wata babbar matsala a jahar
Kaduna.
A kwanakin baya, wasu 'yan bindiga sun sace
tsohuwar ministar Muhalli Laurantia Malam tare
da mijin ta Mista Pious Malam, haka kuma a
makon da ya gabata ne aka sace wani babban
jami'i kungiyar Jama'atul Nasrul Islam tare da
direban sa a hanyar su ta zuwa Kaduna daga
garin Jos babban birnin jahar Pilato.
A watan Yulin da ya gabata ma, an sace jami'in
jakadancin Saliyo, Manjo Janar Nelson Williams
ko da yake an sako shi bayan kwashe kwanaki a
hannun wadanda suka sace shi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An sace tsohon Minista a Najeriya"

Post a Comment