Ba za a hukunta Henderson da Lallana ba

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ba za ta
hukunta 'yan wasan kasar kuma na Liverpool ba
Jordan Henderson da Adam Lallana, kan
rahotannin cewa sun je wani gidan rawa na masu
rawa tsirara a lokacin da suke cikin tawagar 'yan
wasan kasar.
Ana zargin cewa 'yan wasan biyu sun je wannan
gidan rawa ne bayan wasan da Ingila ta ci
Scotland na neman zuwa gasar cin Kofin Duniya,
kuma kasa da kwana uku kafin su yi canjaras a
wasan sada zumunta da Spaniya.
Haka kuma an gano cewa hukumar ta FA ba ta
nemi kyaftin din Ingilan Wayne Rooney ya nemi
gafara ba, kan rahotannin cewa an ga hotunansa
ya yi tatil da giya, bayan wasansu da Scotland, a
wani taron bikin aure a otal din da 'yan wasan
Ingilan suka zauna.
Rooney dai ya nemi gafara a wurin kocin Ingilan
na wucin-gadi Gareth Southgate, kan wannan
lamari.
Kuma dan wasan na Manchester United mai
shekara 31, ya mayar da martani kan wannan
ymadidi da aka yi masa da cewa, an yi ne domin
a ci mutunncinsa.
Sannan ya ce, idan ana son kashe shi ne tun bai
mutu ba, to da sauransa har yanzu, kuma zai ba
wa marada kunya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ba za a hukunta Henderson da Lallana ba"

Post a Comment