Za a tafi zagaye na biyu a zaben fidda gwani

Tsofaffin Firaiministan kasar Faransa biyu za su
fuskanci juna a zaben fidda gwani zagaye na
biyu na tsayar da dan takara a zaben shugaban
kasar da za'a gudanar shekara mai zuwa.
Francois Fillon da kuma Alain Juppé sun zo na
daya da na biyu ne a zagayen farko na zaben da
jam'iyyar Republican ta shirya.
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy
ya sha kaye tun a zagayen farko ne bayan da ya
zo na uku, kuma yana daya daga cikin 'yan
takaran da suka sha kaye a zagayen farko daya
nuna goyon bayan sa ga Mr Fillon a zaben fidda
gwanin da za'a gudanar ranar Lahadi mai zuwa.
Wakilin BBC yace wannan zabe yana da matukar
muhimmanci saboda duk wanda ya lashe shi
akwai yiwuwar shi ne zai zama sabon shugaban
kasar Faransa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Za a tafi zagaye na biyu a zaben fidda gwani"

Post a Comment