Mara ganin da 'ya fi masu ido fasaha

Wani matashi da ba ya gani, mai shekara 25, a
garin Geza da ke yankin Murya ta jamhuriyar
Niger, yana sana'ar tura kudi ta wayar salula.
Ibrahim Mansur bai tsaya nan ba kawai, yana
dawo da layin wayar da ya lalace ko ya
salwanta.
Bugu da kari, matashin yana aikin daukar taki
zuwa gonar mutane, a amalanken shanu.
Ibrahim ya ce " duk abin da mai ido yake yi, idan
na rubuta shi a zuciyata ni ma na fara wannan
abu, to fa kadan mai ido zai kara a kan inda na
tsaya."
Wasu mazauna Geza, garinsu Ibrahim, sun ce
matashin yana yin aikin gona da suka hada da
fardar gyada.
Sannan kuma ya san hagunsa da damansa
saboda ba ya bata idan yana tafiya.
Wani abun mamaki ma shi ne idan har kun taba
yin hannu da Ibrahim, to har abada ba zai manta
da kai ba.
Ibrahim Mansur dai ya gamu da nakasar rashin
gani ne yana dan shekara biyar da haihuwa,
bayan fama da cutar da ke haifar da cin
zazzana.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mara ganin da 'ya fi masu ido fasaha"

Post a Comment