Harin bam ya kashe 'yan Shi'a da dama a Afghanistan

Yan sanda a Afghanistan sun ce akalla mutum
27 ne suka mutu a harin kunar bakin wake da
aka kai a cikin wani masallacin 'yan Shi'a a
birnin Kabul.
Akalla wasu mutum 35 kuma sun samu raunuka
a harin wanda aka kai a masallacin Baqir ul Olum
da ke yammacin birnin.
Wani dan kunar bakin wake ne ya tara da bam
din da ke jikinsa a lokacin da masallacin ya cika
da wadanda ke halartar tarurrukan addu'o'i na
musamman.
Kungiyar masu ikirarin kafa daular Musulunci ta
IS ta ce ita ta kai harin.
Wakiliyar BBC a birnin ta ce wasu mazauna
unguwar sun ce sun ga gawarwaki da dama,
yayin da wasu rahotanni suka ce yara kanana na
cikin wadanda suka mutu.
Ana kuma fargabar cewa watakila a samu
karuwar a adadin mutanen da suka rasu a harin.
Harin na ranar Litinin ya zo ne a lokacin da ake
shirin tunawa da Iman Hussaini, jikan Annabi
Muhammad (SAW).

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Harin bam ya kashe 'yan Shi'a da dama a Afghanistan"

Post a Comment