Rikicin Myanmar: Mutane arcewa zuwa Bangladesh

Daruruwan musulmai 'yan kabilar Rohingya da
suka hada da kananan yara na ta kokarin
tserewa rikicin da ake a Myanmar ta hanyar
tsallaka kan iyakar Bangladesh.
Farmakin da sojoji suka kai a jahar Rakhine ta
Myanmar din, inda da yawan 'yan tsiraru 'yan
kabilar Rohingya ke zama, ya halaka a kalla
mutane dari da talatin a cikin wata guda.
Masu fafutuka da shaidu sun ce an kona
daruruwan gidaje kurmus.
Gwamnatin kasar Burma ta musanta ikirarin,
amma kuma sun ki yadda 'yan jarida na
kasashen waje su je wajan.
Shaidu da jami'an Bangladesh sun ce an harbe
har lahira wasu da suka yi kokarin tserewa zuwa
Bangladesh, yayin da aka tilastawa wasu kuma
komawa gida.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Rikicin Myanmar: Mutane arcewa zuwa Bangladesh"

Post a Comment