Kasar Saudiyya ta fara cika alkawarin biyar diyyar mamata

Hukumomin Kasar Saudiya tare da hadin
gwiwar hukumar mahajjata ta Najeriya sun
mikawa magadan Alhazai goma sha biyu na
jihar Adamawa da suka rasa ransu a
turairainiyar da ta abku lokacin akin hajjin
2015 kaddarorinsu.
Shugaba Buhari tare da sarkin Saudiya
Babban sakataren hukumar kula da jin dadin
mahajjata na jihar Adamawa Injiniya Umaru
Bobboi ya shaidawa majiyar mu cewa maido
da kaddarorin wadanda suka rasun ya dauki
tsawon lokaci ne saboda nazari mai zurfi da
hukumomin suka yi wanjen tantance
wadanda suka rasu da kuma magadansu.
Babban sakataren ya ce darasin da ‘yan
Najeriya musamman jami’an tsaro yakamata
su yi koyi da shi shine na rikon amana da
tsare gaskiya.
Cikin juyayi da tausayi daya daga cikin
magadan Alhaji Lekki ya jinjinawa
hukumomin Saudiya da na alhazan Najeriya
da rikon amanar marayu.
Mutane dai na ganin cewa matakin na
hukumomin Saudiyya suka dauka ya Kara
kyakkawar gurbi dadai da koyarwar addinin
Musulumci.
Bayaga mahajjata goma sha biyu da aka
tantance gawarsu akwai mutane biyu da ba
a ga gawarsu ba gamma aka bada tabbacin
rasuwarsu bayan an dauki sanfarin jin in
‘ya,yansu da name mahaifansu mata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kasar Saudiyya ta fara cika alkawarin biyar diyyar mamata"

Post a Comment