Kaduna: An binne mutum 23 a kabari ɗaya a garin Chawai

Mutum 23 ne aka binne a wani kabari na bai-
daya bayan wani rikici a gundumar Chawai ta
jihar Kaduna a kwanannan.
Wadanda aka binnen na daga cikin mutane fiye
da 30 da suka rasa rayukkansu a cikin rikicin
wanda ya barke tsakanin manoma da makiyaya
kan wata gona a gundumar wadda ke yankin
karamar hukumar Kauru ta kudancin jihar.
Wadannan bayanan sun fito fili ne bayan da
kwamitin wanzar da zaman lafiya a jihar ta
Kaduna ya ziyarci yankin domin gane wa idonsa
abin da ya faru.
Wani wakilin BBC da ya ziyarci yankin tare da
tawagar kwamitin ya ce ko baya ga hasarar
rayukka, tashin hankalin ya haifar da asarar
gidaje kimanin 130.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kaduna: An binne mutum 23 a kabari ɗaya a garin Chawai"

Post a Comment