Zazzabi ya kashe mutum 32 a Niger

Akalla mutum 32 sun mutu tun watan Agusta
sakamakon zazzabin Rift Valley a Niger kamar
yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya
rawaito ma'aikatar lafiyar kasar na cewa.
A wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta fitar, ta
ce annobar ta bazu a yankin Tahoua, inda mutum
230 suka kamu da ita.
Zazzabin Rift Valley dai cuta ce da sauro ke
yadawa - hasali ma dai cutar dabbobi ce kamar
awaki, akuyoyi da kuma rakuma.
Sai dai makiyaya da masu kula da dabobbi suna
da hadarin kamuwa da cutar kamar saboda zai
iya yaduwa ta hanyar taba jinin dabba ko kuma
idan sauron da ya kuma da cutar ya cije mutum.
Alamomin cutar na farko da ke bayyana a jikin
mutum sun hada da zazzabi da ciwon kai wanda
zai iya tsananta zuwa fitar da jini daga dadashi
da hanci a wasu lokutan ma mutum ya shiga
halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce yawan
mace macen da ake yi ya ragu da kashi 50 cikin
100 a cikin watanni uku da suka wuce zuwa
kashi 14 cikin 100, sakamakon wani shirin wayar
da kan jama'a na gwamanti, da ya bukaci mutane
su rika birne gawarwakin dabbobi tare da yin
takatsantsan wurin mu'amala da matattun
dabbobi da kuma gujewa shan madara wadda ba
a gauraya ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zazzabi ya kashe mutum 32 a Niger"

Post a Comment