Birnin New York na cikin tsoron mulkin Trump - Blasio

Magajin garin birnin New York Bill De Blasio ya
ce ya fada wa Donald Trump cewa al'umomin
baki da ke birnin na cikin fargabar abin da
zamansa shugaban kasa zai jawo musu.
Bayan wani taro wanda ya kira na fada wa juna
gaskiya, Mr. Blasio dan jam'iyyar Demokrat, ya
ce ya nuna wa Mr. Trump cewa iyalai masu
dimbin yawa za su tarwatse sakamakon shirinsa
na tasa keyar baki zuwa kasashensu.
Bayan da ya ci zabe dai Mr. Trump sai ya ce
babban abin da yake shirin yi shi ne kau da ko
tsare kimanin bakin haure miliyan uku wadanda
ke tarihin aikata wani laifi.
Sai dai tuni jami'an manyan biranen Amurka suka
nuna rashin amincewa da wannan shawarar tasa,
sai kuma yanzu magajin garin birnin na New
York, ya ce birnin zai yi duk iya abin da zai iya
domin kare ma'aikatan da ba su da takardun
iznin zama kasar da ke zaune a can daga a tasa
keyarsu zuwa kasashensu.
Birnin na New York na da kusan ninki uku sama
ga adadin bakin aka kayyade kowane birni a
kasar ya tsugunar kuma a baya Mr. De Blasio ya
sha alwashin goge sunaye ma'aikatan da ba su
da takardun iznin zama kasa daga naurorin
adana bayanai, domin hana a zakulo su.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Birnin New York na cikin tsoron mulkin Trump - Blasio"

Post a Comment